Kamar jamb,bude account na banki da dai sauransu, kafin mu tafi ga darasinmu gadan gadan zamu É—an yi gajeran bayani akan muhimmancin Gmail dama amfaninsa
Da farko menene EMAIL
A turance izan aka ce EMAIL a na nufin Hanyar aika sakonni daga wani wuri zuwa wani wuri ta hanyar amfani da na'ura ko ince lantarki
Dakwai kamfanoni da dama dake bada daman mallakar Email cikinsu kuwa akwai gmail,yahoomail,hotmail e.t.c
In Allah ya yarda muddin kuna tare da mu duk zamu yi maku bayani dalla dalla akan yadda zaku bude Email da kamfanoni da muka lissafo a nan sama, amman bari mu fara da Gmail
Muhimmancin Email
Kamar yadda na fada maku ne a sama cewa Email yana da matukar muhimmanci domin kuwa yanzu babu shafin da zakaje kayi register ko joining nasu batare da ka sanya email naka ba don su rika aiko maka da sakonni,
Ku dau misali da JAMB, sanin kanku ne dole sai mutum yana da Email address sannan ake bude masa jamb, to amman kun taba yin tunanin dalilin ya sanya ake bukatar Email a Jamb,
Babban dalilin daya sanya jamb ke bukatar Email naku shine don turo maku da sakonni, in baku manta ba na sanar daku Amfanin email dama kenan turo da aika sakonni ta internet, ta email naku jamb zasu na tura maku duk wasu informations daya danganci jamb account naku bama tare da kunje portal nasu ba
Kuna da sanin da cewa a facebook izan kuka sanya Email naku zasu rika turo maku da duk wani activities da kukayi a facebook ta Email inbox naku, a takaice dai Email kamar SMS yake ta wani fannin ma yafi SMS amfani dun shi international ne a kowacce kasa zaka iya amfani da ita sannan daga kowacce kasa za'a iya turo maki da sako ta cikinta kuma zaku iya turawa
Menene GMAIL
Gmail na nufin GOOGLE MAIL wato kamfanin aika sakonnin EMAIL na Google kusan a duk gabadayan kamfanonin Email na duniya mutane sunfi amfani da gmail, sannan koda ma ace mutum yana amfani da yahoomail ko hotmail kai kuma kana amfaninda gmail zaka iya tura masa sako babu damuwa
Yadda zaku bude account da gmail
Da fark kubi link dinnan
https://accounts.google.com/signup/v2/webcreateaccount?flowName=GlifWebSignIn&flowEntry=SignUpZai kaiku wani wuri kamar haka
Sai ku cika form din
A akwatin farko zaku sanya sunanku kamar yadda kukaga na saka
Akwati na biyu kuma sai ku sanya sunan babanku
Akwati na uku kuma sai ku rubuta yanda kuke da bukatan adireshin gmail din ya kasance misali kamar shuraihu009@gmail.com
Akwati na hudu kuma wurin saka password ne (kalmar sirri)
Akwati na biyar zaku maimaita kalmar sirrin da kuka sanya a akwati na hudu don tabbatar da kun saka daidai
Daga nan sai ku danna maballin next zai kawoku wanni shafi makamancin hoton kasannan
Akwati na biyu kuma zaku sanya Recovery Email Naku
Recovery Email: na nufin wani Email wanda yake naka ko na Abokinka, koda an samu akasi ka manta password din wannan email din naka zasu bukaci ka sanya Recovery Email din daka saka a anan ko kuma izan ana kokarin ai maka hacking Gmail in mutum baisan Recovery Email naka ba dole yayi hakuri,Izan bakwada da wani Email din sai kubar wurin empty batare da kun saka komai ba
Abu nagaba shine Shekarun haihuwarku,
Da farko zaku saka watanni a karkashin akwatin month, sai ranan da aka haifekun a karkashin akwatin days shekarun kuma akarkashin years
Misali: 11 - 04 - 2000
Abu nagaba shine ku zabi jinsinku,
Abun lura: kada kuyi gangancin saka shekarun karya wanda bana haihurwarku ba, domin kuwa a nan gaba zasu iya bukatar da ku dora government ID naku
Bayan kun gama saita duk wannan sai ku danna next
A wannan shafin zasu bukaci ku sanya nambar wayarku izan kuka saka zasu turo muku da verification code ta SMS
Sai kuyi minimize kuje inbox naku ku kwafe code din sa'annan ku dawo ku zuba shi a wurinda suka bukata
Zasu kawoku wurin dokokinsu kuyi kasa ku danna Agree Kai tsaye zasu kawo ku profile naku kaman haka
A nan zaku iya canza duk wasu bayanan account din kama daga kan hoto,suna,ranar haihuwa da dai sauransu
Anan muka kawo karshen wannan darasi mun barku lafiya
Duk mai tambaya sai ya ajjiyeta a comment








Comments