Bayani akan USSD CODE na bankunan Nigeria da sunayensu
TechnologyAssalam ayau zamu duba gefen bankunan Nigeria gaba daya, inda zamuyi bayani akan USSD CODE nasu da amfanin shi.
Hanyoyin Ajiya da ciran kudi a banki a Nigeria ya zamto mai saukin sauƙaƙawa a yanzu duk a ta dalilin USSD CODE.
Kowanne banki da kuka sani a Nigeria nada USSD CODE ko ince bank transfer code hakanan kuma duk wanda ya bude account da banki yana da daman yin amfani USSD CODE na bankinsa
In kana amfani da UBA bank, hakan na nufin kana da cikakkiyar damar amfani da USSD CODE na su don saukake tura kudi zuwa wani account din ta hanyar wayarka
Koda saving account ne ka bude ko current account kana da cikakkiyar damar amfani da USSD CODE na bankinka don saukake tura kudi ta hanyar amfani da wayar salula
Zamu lissafo maku Bank transfer code (USSD CODE) na kowanne banki dake Nigeria a nan kasa ammana kafin nan bari mu sanar daku ko menene USSD CODE da muhimmancinsa kana da amfaninsa
Menene USSD CODE KO BANK TRANSFER CODE
bank transfer code wani tsari ne mai sauri da sauki kana mai tsatstsauran tsaro da zai baku damar sarrafa asusunku na banki cikin awanni 24 a rana guda, kana kwanaki bakwai 7 a mako guda ta hanyar amfani da wayoyinku batare da kun saka DATA ba,
Kamar yadda kukaji nake ta fadin USSD CODE tsarine da aka fitar din saukaka hadadan banki, Wanda zaku iya amfani da da kowanne lokaci babu ruwansa da dare ko safiya ko karfe hudun dare ne zaku iya amfani da shi, hakanan batare da kunje banki ba kuna zaune a gidajenku cikin kwanciyar hankali kuna lallatsa wayoyinku zakuyi transfer din kudi zuwa wani account din batare da kunje kunbi sahun layi a banki ba don yin transfer ko makamancin sa, hakanan kowanne rana zaku iya amfani da shi babu ruwansa da ranakun hutu asabar da lahadi, sannan wani abun dadin ma shine baya amfani da internet bare azo ga batun cin data.
AMFANIN USSD CODE
Da wannan USSD CODE din da muke magana akai zaku iya yin dukkan abubuwan da zan lissafo a nan kasa:
- Zaku iya siyan kati (Recharge card)
- Zaku iya siya wa wasu ma katin (Recharge card)
- Zaku iya duba kudadenku na banki (balance)
- Zaku iya tura kudi zuwa wani asusun (transfer)
- Zaku iya biyan bill (bill payment)
- Zaku iya canza PIN na ATM card din ku
- Zaku iya siyan data
- Zaku iya siyan ma wasu data
So koda kunga wani abu makamancin hakan na gaba ina fata zaku gane cewa USSD CODE ne
JERIN USSD CODE NA GABADAYAN BANKUNAN NIGERIA
- UBA BANK code nasu *919#
- FCMB code nasu *329#
- ACCESS BANK code nasu *901#
- WEMA BANK code nasu *945#
- FIRST BANK code nasu *894#
- POLARI (skye) BANK code nasu *833#
- GTBANK code nasu *737#
- ZENITH BANK code nasu *966#
- ECO BANK code nasu *326#
- STANBIC IBTC BANK code nasu *909#
- DIAMOND ACCESS BANK code nasu *426#
- FIDELITY BANK code nasu *770#
- STERLIN BANK code nasu *822#
- UNITY BANK code nasu *7799#
- JAIZ BANK code nasu *389*301#
- KEYSTONE BANK code nasu *7111#

