Insha Allah yau darasinmu zai tattauna ne akan yadda zaku samu MB 500 ko 100 wasu ma zasu iya samun 600 a layin MTN ta hanyar amfani da MY MTN APP
Kusan kowa yasan manhajar (application) din MY MTN APP, manhajar mymtnapp dai zai baka daman sayen data, sayen katin waya ta banki da sauransu, sannan izan ya kasance baka taba amfani da manhajar ba da zarar ka bude zasu baka kyautar MB 500
Yanzu kuma da kwai wata kyautar MB 100 da suke bayarwa a wannan watan, wanda koda ace ka taba amfani da application din ko baka taba ba da zarar ka bude zasu baka zunzurutun MB har guda 100
Izan kuwa baka taba budewa ba yakasance wannan ne karon farkonka da budewa toh zasu baka MB 500 na budewar da kai sannan da MB 100 kyautar da suke bayarwa na wannan wata kaga izan ka hada ka samu MB 600 kenan
YADDA ZAKA SAMU DATAN
Da fari ka tabbata wayarka Android ce
Sannan sai ku downloading mymtnapp anan kasa
Bayan kun download na app din sai ku install sannan ku bude, zasu nemi ku sanya nambar wayarku bayan kun saka zasu turo da message mai dauke da kalmar sirri na lokaci guda (one time password) ta simcard din sai ku kwafe nambobin guda shida 6 ku dawo application din ku zuba take zasu bude application din.
In baku taba budewa ba a saman app din zaku ga ansaka
YELLO! YOU HAVE BEEN REWARDED WITH 500 MB FREE DATA
Sai ku danna kan CLICK HERE TO ACTIVATE IT
Daga nan zasuyi maku message akan sun baku data 500mB kyauta sai ku danna *559*4# don duba data din izan kuka duba zakuga 600MB harda kyautan da sukeyi
Izan kuwa ka taba budewa a saman zakaga an rubuta
YOU HAVE BEEN REWARDED WITH 100 MB FREE DATA
sai ku danna kan CLICK HERE TO ACTIVATE IT atake zasu baku mb 100 sai ku danna *559*4# don duba MB din
Duk Abunda baku gane ba ku yi tambaya a comment
Dakwai wani darasinma na samun data 2GB a mtn kyauta kuma kullum

Comments