Assalamu'alaikum da yardan Allah yau zamu fara darasi akan yadda zaku gina website naku na kanku a shafin gina website (webbuilder) na wapkiz.
Wapkiz dai webbuilder ne da zai baku daman hada hadadden website a kyauta sannan kuma ku samu kudi da website din, kusan yawancin webmaters da kuke gani yanzu sun fara ne da kananun webbuilder irinsu wapkiz,xtgem da wapka, mywapblog da dai sauransu kafin su koma blogger da WordPress
Ayanzu dai wapkiz shine best free webbuilder in the world duba da yadda yake da sabbabbin features kuma yake baiwa mutum daman saka tallan Adsense sabanin wasu webbulider din da vasa taba yadda a sanya tallan adsense a shafukan da aka kirkira da builder nasu.
Zamu fara darasinne akan yadda zaku hada Download website, wato shafin yanar gizo gizo da ake dora fayil fayil, irinsu wakoki,vidiyoyi,aplications da dai sauransu
Da fari kuje browser naku ku rubuta http://wapkiz.com zai kaiku shafin sai ku taba kan register dake a sama
Daga nan zai kawoku wurin yin register din zakuga form sai ku cika da bayananku kaman
Zai sake kawo ku wani wurin inda za a bukaci ku sanya sunan website din da kuke son budewa da short description nashi da kuma category na shafin, a wurin subdomain ku zabi wapkiz.com tayadda za arunga ziyartar shafinku kamar haka www.shafinku.wapkiz.com .
Ku danna maballin Apply sannan Zai dawo daku shafinnaku inda zakuga shafin a ciki design mai kyau
Sai ku tsumayemu a kashi na gaba wanda zamuyi bayanin yadda zaku dora wakoki da vidiyoyi da kuma yadda zaku bude category wa kowanne fayil
Sai ku tsumayemu a kashi na gaba wanda zamuyi bayanin yadda zaku dora wakoki da vidiyoyi da kuma yadda zaku bude category wa kowanne fayil







Comments