Assalamu'alaikum jama'a
A rayuwar da muke ciki a yanzu technology ya samu karbuwa sosai a duniya, mutane da dama yanzu zaka samu sun aminta da ajiyan kudi a banki bisa kan su ajje a gida don kuwa suna da tabbacin cewa banki yafi gida tsaro
A cikin kashi dari na mutane zaku samu kashi casa'in da tara na da asusun (account) banki wanda suke ajjiye kudadensu a can,
Hakanan a cikin kaso dari na wayanda suka bude asusun banki zaku samu kaso casa'in da tara duk da katin ATM suke amfani wurin cirar kudadensu a banki, duk da cewa a kwai masu amfani da cheque da withdrawal slip, ammana masu amfani da ATM sun fi su yawa,
Katin ATM yana zamantowa tamkar shine akalar bankinka domin kuwa a kowanne lokaci izan ku ka bushi iska zaku iya tafiya ku ciri kudi, koda kuwa ace sha biyun dare ne, sabanin cheque da shi dole sai lokacin da banki ke aiki sannan zaka ciri kudi da shi,
nadaga cikin babban dalilin dayasa mutane da dama suka fi amfani da ATM bisa kan cheque
Tofa sai dai dakwai babbar kalubale daya tun karo mu gadan gadan na yaduwar wasu bata garin mutane wai su (yahoo boys) ko (fraudster) duka sunayensu ne, wayannan mutane suna amfani da ATM din mutum su ciri kudaden bankinsa batare da saninsa ba hakanan wani lokacin ba baza ka ga Alert na an debi kudin ka ba sai dai kawai ka farga kaga asusunka babu taro bare sisi.
Yahoo boys na samun daman yin hakanne ta hanyar samun bayanan dake rubuce a jikin katin ATM dinku, wanda da zarar sun ga bayanan shikenan sun samu account naka a hannunsu, sai yadda suka ga dama
Insha Allah zan baku hanyoyi guda goma wayanda na tabbata muddin kuka bi sannan kuka kiyaye da yardan Allah macuta Yahoo boys bazasu samu Nasara akan ku ba
1. Kuyi kokari ku rika sabunta bayanan bankinku akai akai musamman ma Nambar waya,Adireshin Email, Addireshinku da sauransu wanda kuka baiwa bankin yayin register naku, hakan zai taimaka wa bankin matuka wurin sanar daku duk wani shiga da ficen kudi a asusunku
2. Ku kare kanku daga sharrin yan kutse madan datsa, nasu satar bayanan mutane, dakwai darasin mu da mukayi akan hakan yana da kyau ku karanta shi ga darasin nan YADDA ZAKU KARE KANKU DAGA YAN YAHOO BOYS

Comments